Dan Shekara 32 Ya Amsa Laifin Yiwa Yarinya ‘Yar Shekara 8 Fyade A Minna

Wata Kotun Majistire Mai Mataki na 1 ranar Laraba ta dage yanke hukunci bayan da wani mutum mai suna Ayuba Salihu dan shekara 32 da haihuwa ya amsa laifin yiwa wata yarinya ‘yar shekara takwas da haihuwa fyade.

An kama mai laifin wanda kawo yanzu ba a san adireshinsa ba, bisa laifin aikata fyade.

Mai Gabatar da kara Mr Abdullahi Mayaki na Hukumar Kula da Hakkin Kare ‘Yancin Yara ta jihar ya shedawa kotun cewa lamarin ya faru ne ranar 31 ga watan Agusta kusa da kasuwar Gwari a Karamar Hukumar Chanchaga.

A cewar ta Mayaki wanda ake zargin ya yaudari yarinyar wadda ‘yar makarantar firamare ce zuwa kasuwa da N100 kafin aikata masha’ar da ita.

Wannan laifi dai ya saba da Sashi na 18, Karamin Sashi na 2 na Kundin Dokokin Kare ‘Yancin Yara ta Jihar Nijan.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya rawaito cewa laifin ka iya sawa a yankewa mutum hukuncin daurin rai-da-rai a gidan kaso

Babban Alkalin Majistirin Hassan Muhammed da ya kama wanda ake zargi da laifin ya daga karar zuwa 12 ga watan Satumba don zartar da hukunci

Ya ce daga karar zai bawa mai shigar da karar damar samun bayanan alkalumman dawainiyar ganin likita da iyayen yarinyar sukayi kawo yanzu.

435total visits,1visits today


Karanta:  'Ko Buhari Ya Tambaye Su Aikin Yi Nawa Aka Samar?'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.