Dangote ya bawa ‘yan kasuwar Kano Naira Miliyan 500

Shugaban gamayyar kamfanunuwan Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya sanar da bayar da gudummawar Naira Miliyan 500 ga wadanda gobarar kasuwannin Kano suka shafa a shekarar da ta gabata.

Aliko Dangote ya sanar da hakan ne a yayin taron hada gudummawa ga ‘yan kasuwar a dakin taro na Coronation Hall wanda ke fadar gwamnatin jihar Kano a yau.

A shekarar data gabata ne aka kafa kwamitin gidauniya domin tallafawa ‘yan kasuwar wanda Aliko Dangote ya kasance a matsayin shugaba.

Da yake jawabi a wajen taro, Dangote ya yi kira ga al’umma da su bayar da gudummawa domin tallafawa wadanda suka rasa dukiyoyin su.

Kakakin Majalisar Wakilai na Tarayya Yakubu Dogara wanda Hon Alhassan Ado Doguwa ya wakilta ya bayyana bayar gudummawar Naira miliyan 5, sai kuma ‘Yan Majalisar wadanda ke wakiltar kananan hukumomin Jihar Kano sun bayar da gudummawar Naira 500,000 kowanne su. Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa ya bayar da Naira miliyan 10.

‘Yan Majalisar Dokokin jihar Kasa kowannen su ya bayar da gudummawar Naira 100,000, inda kakakin majalisar ya bayar da Naira miliyan daya.

A wani bangaren kuma Sanata Kabiru Gaya da Sanata Barau Jibrin sun bayar da Naira miliyan 3 kowannen su.

Taron dai ya samu halartar jihohin Arewa inda jihar Katsina ta samu bayar da gudummawar Naira miliyan 10.

3377total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.