Dangote Zai Gina Katafaren Kamfanin Siga a Jihar Neja

Kamfanin Dangote ya sanya hannu kan wata yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Neja don gina katafaren kamfanin siga na kimanin Naira biliyan 166 a jihar.

Kamfanin Dangote ya sanya hannu kan  wata  yarjejeniya da Gwamnatin Jihar Neja don gina katafaren kamfanin siga na kimanin Naira biliyan 166 a jihar.
Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote shi da kansa ya sanya hannu a madadin kamfaninsa shi kuwa Gwamna  Abubakar Sani Bello ya sanya hannu a madadin jihar Neja.
Da yake jawabi jim kadan da sanya hannun kan yarjejeniyar, Shugaban Kamfanin Dangote ya ce kamfanin zai samar da guraben ayyuka fiye da dubu 15 a jihar.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta sanya kamfanin ya rika samar da gonar rake mai fadin hekta dubu 16 a Karamar Hukumar Lavun da ke jihar.
Ya ce aikin zai hada da kafa katafaren kamfanin siga da samar da man etanol da abincin dabbobi.
Ya ce katafaren kamfanin samar da sigan zai rika samar da sigan da ya kai tan dubu 160 na gundarin siga zalla.

 

Asalin Labari:

Aminiya

674total visits,1visits today


Karanta:  Ni ban bai wa 'yan majalisar Kano cin hanci ba – Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.