Darajar Naira ta karu N359.7 a dala. Kudin ajiyar Najeriya ya kai dala biliyan 31.35

Darajar Naira a jiya ta samu dagawa a karo na farko a gangaren ‘yan kasuwar sanya hannun jari sakamakon karuwar kudade na dalar Amurka da babban bankin kasa yake bayarwa a duk mako.

A wani bangare, babban bankin na kasa ya bayyana cewar kudaden ajiyar Najeriya na kasar waje ya karu da dala miliyan 392 zuwa dala biliyan 31.375 a makon daya gabata daga dala biliyan 30.965 a Juma’ar data gabata kafin nan.

Alkaluma dai a halin yanzu sun nuna farashin canjin ya sauka izuwa Naira 359.65 a dalar Amurka daga 362.38 a ranar Alhamis din data gabata.

Wannan ya nuna cewar Naira 2.69 ya ya ragu inda Naira ta samu karin daraja akan dalar ta Amurka sakamakon karuwar Naira da 6.81 akan dallar.

Daguwar farashin ya auku ne sakamakon karin kudaden da babban banki kan bawa masu hada hada da kashi 154 izuwa dala miliyan 236.38 daga dala miliyan 93.21 a ranar Talatar data gabata.

Cinikayya dai a yanzu ta kai dala miliyan 446.95 a wannan satin.

391total visits,1visits today


Karanta:  Fatan ’yan kasuwar Kano kan tallafin gobara

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.