Dawowar Buhari ta karo karfin gwuiwa – Gwamna Bello

Gwamnan jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya bayyana cewar dawowar shugaba Muhammadu Buhari daga birnin Landan inda ya shafe kwanaki yana jinya wata babbar nasara ce a Najeriya wanda zata karfafawa ‘yan kasa gwuiwa wajen yin aiki tukuru da kuma tabbacin gyaran kasa Najeriya.

Gwamna Abubakar Sani Bello wanda ya ziyarci shugaba Buhari a Landan a kwanakin baya ya bayyana cewa shugaban ya shaida musu cewar addu’oi da fatan alkairi da al’ummar Najeriya sukeyi kan karfafa masa gwuiwa wajen dawowa don ci gaba da ayyukan da aka doru akan su.

“Dawowar Shugaba Buhari wata dama ce ta tabbatar da cewar akwai yanayi mai kyau a gaba inda muke saka ran kasar mu Najeriya zata haskaka. ‘Yan Najeriya kan kalli shugaba Buhari a matsayin uba, wani jagora wanda ya doru akan gina kasar mu ta gado. Don haka alamun sun nuna cewar yadda al’umma suke ta dokin dawowar sa wani abu ne da zai kai kasar mu ga nasara”.

Ya kara da cewa dawowar tasa wata abace da zata tsoratar da masu yada jita jita da kuma wadanda burinsu ace ma labarin yasha ban-ban. Maimakon ace sunayi masa kyawawan fata, burin su shine kana ya dawo da ransa.

Asalin Labari:

LEADERSHIP

4859total visits,1visits today


Karanta:  Bikin Ranar Zaman Lafiya Ta Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.