Dole Ne Kananan Hukumomi Su Samu ‘Yanci – NULGE

Bayan samun nasarar amincewa da cin gashin kan kananan hukumomi a majalisun tarayya yanzu kungiyar ma'aikatan, NULGE tace zasu cigaba da fafutikar tabbatar da 'yancin a duk jihohin kasar 36.

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya ta kafa kwamitin shawo kan majalisun kasar 36 domin amincewa da cin gashin kan kowace karamar hukuma.

Kafin kananan hukumomin su samu ‘yanci ana bukatar amincewar a kalla jihohi 24 ko kashi biyu cikin uku na jihohin 36.

Yanzu jihohi ne ke shirya zaben kananan hukumomi da jagorantar harkokin kudi lamarin da shugaban NULGE Kwamred Ibrahim Khalid ya kira aikin babangiwa. Yace zasu cigaba da fafutika cikin lumana a duk jihohin kasar.

Abun da kungiyar zata sa gaba shi ne wayar da kawunan ma’aikatan kananan hukumomin tare da hadawa da addu’oi da ziyarar sarakunan gargajiya da zuwa majalisun jihohi.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1131total visits,1visits today


Karanta:  Samar Da Aikin Yi a Yankunan Igbo Zai Iya Kawo Zaman Lafiya - Kwararru

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.