Donald Trump Na Fuskantar Suka Daga ‘Yan Jam’iyyarsa

Ana ci gaba da samun rashin goyon baya ga hukuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na yiwa tsohon babban jami'in 'yan sandan jihar Arizona afuwa.

Ana ci gaba da samun rashin goyon baya ga hukuncin da shugaban Amurka Donald Trump ya yanke na yiwa tsohon babban jami’in ‘yan sandan jihar Arizona afuwa, bayan da aka same shi da laifin nuna wariya.

Kakakin majalisar Wakilan Amurka Paul Ryan ya bayyana cewa, bai goyi bayan shawarar da shugaba Donald Trump ya yanke ta yiwa tsohon babban jami’in ‘yan sandan jihar Arizona Joe Arpaio afuwa ba, kasa da wata guda bayan samunsa da laifin nuna wariya.

Mai Magana da yawun kakakin majalisar, Doug Andres ya fada a wata sanarwa cewa, “Jami’an kiyaye doka da oda, suna da hakki na musamman, na kare kowa a Amurka. Bai kamata mu kyale wani ya yi tsammanin, ahuwar na nuna cewa, yanzu an dage wannan nawayar ba.

Dukan ‘yan majalisar dattijai biyu dake wakiltar jihar Arizona, John McCain da Jeff Flake suma sun kushewa wannan yunkurin.

A sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ranar jumm’a da yamma tace, Arpaio, “ya shafe dukan rayuwarsa yana kare al’umma daga miyagun laifuka da kuma shiga kasar ba tare da izini ba. Kuma yanzu Jami’in dan sanda Joe Arpaio mai shekaru tamanin da biyar a duniya, bayan shafe sama da shekaru hamsin yana yiwa kasa aiki, ya cancanci shugaban kasa ya yi masa ahuwa.

Asalin Labari:

VOA Hausa

613total visits,1visits today


Karanta:  Rasha ta Bukaci Amurka Data Dawo Mata da Gidajen Ta

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.