Dubban ‘yan jam’iyar APC sun cika da buri

Dubun-dubatar magoya bayan jam`iyyar APC mai mulki a Nigeria na ci gaba da zaman jiran-tsammani.

Wannan ya biyo bayan ikirarin da shugaban kasar ya yi na kara yawan ministoci da nade-naden wasu mukamai ta yadda `yan jam`iyyar za su ji ana damawa da su.

Abin tambaya shi ne ko gaggauta yin nade-naden zai kara wa shugaban kasa da jami`iyyar APC tagomashi a cikin lokacin da ya rage wa`adin mulkinsa ya cika?

Miyau ya karyo a bakunan `yan jam`iyyar APC da dama tun lokacin da shugaban Muhammadu Buhari ya yi albishir da cewa zai fadada tabarma siyasa ta hanyar kara yawan ministoci da nadin shugabannin da mambobin hukumomin gudanarwa ga wasu ma`aikatun gwamnati.

 

Tun bayan mako uku da wannan alwashi da shugaban kasar ya dauka, amma shiru kake ji. Kodayake wata ruwayar na cewa anan can ana ta kokarin darje wadanda suka fi dacewa da mukaman ne.

Sai dai magoya bayan shugaba Buharin na ganin cewa ya kamata a hanzarta cika wa `yan jam`iyyar burinsu don kauce wa zargin da wasu ke yi cewa sun tura mota ta bar su da kura.

Abdulmajid Danbalki Kwamanda wani jigo ne a tsakanin magoya bayan shugaban kasar, wanda yace bas hi da kwadayin mukami, amma hanzarta yin nadin na da fa`ida.

A gwamnatin shugaba Buhari dai an dade ana hadirin nadin mukamai, amma a karshe kan zama holoko, wai hadirin kaka in ji `yan magana.

Tun gwamnatin shugaba Buhari ba ta wuce shekara guda da kafuwa ba aka yi ta sa ran zai yi garambawul ga majalisar zartarwa tare da karkade wasu mukarrabansa, wadanda ake zargin amfaninsu kadan ne da kuma nadin shugabannin hukumomin gudarwar wasu ma`aikatu, amma babu abin da ya sauya in ba da tsohon sakataren gwamnati Babacir Lawal da aka tube wa rawani bisa zargin aikata almundahana.

Karanta:  Za a halatta kananan matatun mai a Naija Delta

Ganin cewa tafiya ta yi nisa har fara hangen zaben shekara ta 2019, Dr Said Ahmad Dukuwa masanin kimiyyar siyasa a jami`ar Bayero ta Kano, ko kwalliya za ta biya kudin sabulu idan shugaban kasar ya yi nade-naden? Ya ce mai iya kasance hakan.

Wasu `yan jam`iyyar APCn dai na da ra`ayin cewa ya kamata a ba wa gwamnoni damar mika sunayen mutanen da za nadawa mukaman, amma wasu masana na ganin cewa zai fi kyau a sakam ma shugabannin jam`iyya ragama, kasancewar su fi kowa sanin `yan ga-ni-kashe-nin jam`iyya da masu kishin rayata.

Asalin Labari:

BBC Hausa

1719total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.