EFCC Ta Gano Naira Milyan 300 Cikin Wata 4 A Shiyyar Oyo.

Mataimakin shugaban hukumar a shiyyar kazeem Hussein ne ya bayyan ahaka a wani taron manema labarai.

Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa, EFCC, shiyyar jahar Oyo ta gano Naira milyan 300 cikin watanni hudu da suka gabata.

Mataimakin shugaban hukumar reshen jahar Oyo Kazim Hussein, shine ya bayyan haka lokacinda yake magana da manema labarai kan ayyukan hukumar a yankin.

Mr. Kazeem yace cikin wadanda hukumar ta sa a gaba a ayyukanta, sun hada da mazambata ta yanar gizo, da masu cuta ta bankuna da rikicin filaye.

Mr. Kazeem yace hukumar ta sami kararraki 430, ta kama mutane har 200, sannan ta gabatar da kararraki gaban kotu guda 50.

Daga nan yayi kira ga jama’a su fahimci cewa yaki da cin hanci da rashawa ba aiki ne na jami’an gwamnati kadai ba, tilas sai jama’a sun hada hannu da su, domin a samu nasara a wannan yaki.

Asalin Labari:

VOA Hausa

661total visits,1visits today


Karanta:  Sojin Nigeria 'sun kai samame' ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.