EFCC ta sake bankado N 47.2b da $487.5m mallakar Diezani Madueke

Hukumar Yaki da cin hanci da rasava tare da yi wa tattalin kasa zagon kasa, wato (EFCC) ta sanar da cewar ta bankado wasu zunzurutun kudi har Biliyan N47.2  da kuma Dala Miliyan $487.5 tare da kadarori mallakar tsohuwar Ministar albarkatun mai ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke.

“Wannan ya biyo bayan kwakkwaran bincike da ma’aikatan hukumar EFCC,”  Wasu ma’aikatan hukumar yaki da cin hanci da rashawa su biyu, suka bayyana a wata makala da suka aika jaridar PREMIUM TIMES.

Har ila yau, ana bincikar tsohuwar ministar da laifin cin hanci da fitar da kudin sata  a kasar Amurka da Ingila. A wani binciken samame da aka kai a daya daga cikin gidajen Madam Alison – Madueke a Abuja, an gano akwatuna shake da gwala-gwalai, tagulla, azurfa, lu’u-lu’u da kuma wasu makudan kudade na kasar Ingila.

Baya ga wadannan gwala-gwalai, hukumar ta kara binciko wasu makudan kudade kusan Biliyan N47.2 da kuma Dalar Amurka $487.5  tare da wasu kadarori mallakar tsohuwar Ministar ta gwamnatin Goodluck Jonathan.

 

 

 

 

Asalin Labari:

Premium Times, Muryar Arewa

2636total visits,1visits today


Karanta:  Wadanne Batutuwa Buhari ya Taras a Nigeria?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.