Gwamna El-Rufai ya samar da sabbin kayan aiki a babban asibitin Kafanchan

Gwamnatin jihar Kaduna, karkashin jagoracin Mallam Nasir el-Rufai ta samar da sabbin kayayyakin aiki na zamani a babban dakin shan magani na jihar ta Kaduna dake garin karamar hukumar Kafanchan.

Sanarwar ta biyo baya a yau ta shafin sada zumunta na jihar wanda kanyi bayani akan ci gaban da gwamnatin kan samu a yau da kullum.

Da alama dai sabbin kayayyakin zasu kasance karo na farko da wani babban asibitin dake wajen jihar ya taba samu.

Kayayyakin da gwamnatin ta samar sun hada da fitulu na aiki tiyata da ma wasu manya manyan kayayyaki ta musamman.

Gwamna Nasir el-Rufai wanda ya lashe zaben 2015 da ya gabata a karkashin jam’iyyar APC ya sha alwashin habaka bangaren lafiya a jihar ta Kaduna.

A satin daya gabata ne el-Rufai ya gudanar da taro a garin Kaduna domin nuna farin cikin dawowar Shugaba Muhammadu Buhari daga jinya a garin Landan daga kasar Birtaniyya.

3515total visits,2visits today


Karanta:  An kori 'yan sandan da 'suka wawushe gidan Jonathan'

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.