Etsu na Nupe ya nada Sani Danja ‘Zakin ‘yan wasan Arewa’

Fitaccen Jarumin Kannywood kuma Mawaki Sani Musa Danja ya samu nasarar dafe sarautar ‘Zakin Yan Wasan Arewa’.

Sarautar wadda Etsu na Nupe ya tabbatar masa ta kasance ta hudu a cikin jerin Sarautu tabbatattu wadanda aka nada su ga masu shirya fina-finai na Kannywood a ‘yan shekarun nan.

Sarautar ‘Zakin ‘Yan wasan Arewa’ ta jarumi Sani Danja, ta biyo bayan ta sarautar Sardauna da Sarauniya wadda Mai shirya fina-finai Jamilu Ahmad Yakasai Da jaruma Halima Atete ke rike da su.

Tun farko an bada sanarwar wannan gagarumin al’amari mai tarihi cewar ana gayyatar kowa da kowa, masoya da abokai na jarumin.

Rahotanni sun bayyana cewar, iyalai, ‘yan uwa da awoken harkar jarumin sun halarci bikin wanda aka yi a garin Minna. An kuma hango tsohuwar jaruma kuma uwargidan sabon ‘Zakin ‘yan wasan Arewan, wato Mansurah Isah sanye da kaya na al’ada tana taya maigida murna.

 

Asalin Labari:

Muryar Arewa,

2700total visits,1visits today


Karanta:  Dalilin da ya sa na fito a Barauniya - Hafsa Idris

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.