Fadan Ranar Hawan Daushe: An Gargadi Matasa Kan Rigingimun Siyasa

Kungiyar Matasan Nijeriya (YAN) Sashin Jihar Kano sun gargadi matasa da kada su bari wasu ‘yan siyasa su ringa amfani dasu don haifar da tashin hankali a jihar.

Kiran na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kakakin Kungiyar, Komred Bashir Bello Roba ya sanyawa hannu.

Sanarwa ta ce kiran ya zama dole ne duba da abin da ya faru tsakanin magoya bayan Gwamnan Jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje da magoya bayan wanda ya gada a mulki Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ranar Hawan daushen da aka saba gudanarwa duk shekara

 

An cimma daukan matakin gargadar matasan ne a wani zama na musamman da jigajigan ‘kungiyar daga kananan hukumomin jihar 44 suka gabatar.

Sanarwar ta kara da cewa “Abin Allah wadai ne duba da yadda wasu ‘yan siyasa ke amfani da matasan garin na Kano wajen shirya rikicin siyasa.”

Haka kuma sanarwa tayi kira ga jami’an tsaro dasu dauki matakin shari’a kan duk wanda suka samu da laifi a wannan rikici, inda suka kuma shawarci matasan da su kauracewa duk wani dan siyasar da baya nufin alkhairi ga jihar.

“Muna kira ga daukacin ‘yan uwanmu matasa dasu kauracewa ‘yan siyasar da basa nufin alkhairi ga jihar mu. Haka kuma su kauracewa duk wasu kalaman batanci da zasu haifar da abin Allah wadai a garuruwanmu. Alhakinmu ne mu tabbatar cewa an samu yanayi mai kyau a siyasance, a addinance dama rungumar kabilu mabanbanta don samun dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu,” a cewar sanarwar.

754total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.