Fadan Ranar Hawan Daushe: ‘Yan Kwankwasiyya sun sake shigar da korafi zuwa Hukumar ‘Yan Sanda

Wata tawagar ‘Yan Jam’iyar APC tsagin Kwankwasiyya daga Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Rabiu Suleiman Bichi sun sake shigar da sabon korafi jiya zuwa Hukumar ‘Yan Sanda kan rikicin kwananan da ya faru tsakaninsu da magoyan bayan Gwamnan Jihar Abdullahi Umar Ganduje

Da yake Magana a madadin tawagar bayan shigar da korafin, tsohon Kwamishinan jihar kan harkokin gwamnati cewa yayi dole ne Hukumar ‘Yan Sanda ta binciki rawar da Kwamishinan ‘Yan Sandar Jihar, Alhaji Rabiu Yusuf ya taka a fadan da ya faru ranar Asabar din data gabata lokacin bukukuwan babbar sallah.

Yace a bayyane take cewa Kwamishinan ya marawa Gwamna Ganduje baya inda yayi zargin matakin da ‘yan sandan suka dauka na hurawa mambobin kwankwasiyar da sukayi shigar fararen kaya da jajayen huluna barkonon tsohuwa a ranar hawan daushen.

Ya kuma yi korafin cewa kwamishinan ‘yan sanda yaki yarda ya gana dasu lokacin da sukayi kokarin ganawa da shi.

“Muna son Hukumar ‘Yansandan su kalli korafin mu da kyau. Muna son hukumar ta ‘yan sanda su binciki wannan korafin wanda yafi muhimmanci kan wancan korafin da muka shigar. Mun zo nan don ayi mana adalci. A zahiri take cewa an zalunce mu. Mutanenmu sun ji raunuka iri daban-daban.

“Mu mutanene masu son zaman lafiya. Muna kuma cusawa mutanenmu son zaman lafiya. Ba zamu yarda da rikici ba. Amma kuma hakan nada iyaka.

“Mun shigar da wannan korafin ne don bama son yanayin da zai kai muna kare kanmu. Muna da yawa da karfi na zahiri da zamu iya kare kanmu. Amma dai mun kauracewa yin hakan.”

Karanta:  Buhari na Kokarin Dinke Rikicin APC

Da yake mayar da martini, Shugaban Hurda da Jama’a da Manema Labarai na Hukumar wato Mr Ikechukwu Ani, cewa yayi hukumar ta karbi rahoton kuma ya bada tabbacin cewa Mai Shari’a Olufunmilola Adekeye wanda ke jagorantar Kwamatin Korafe-Korafe kan Ayyukan ‘Yan Sanda zai gudanar da bincike kan lamarin kuma zai tabbata cewa gaskiya tayi halinta.

Ani, wanda yayi magana a madadin kwamitin cewa yayi tun da fari sun zauna kan korafin farko da aka shigar ranar 28 ga watan Agusta, 2016 inda suka gudanar da wasu bincike-bincike kan lamarin.

Ya bayyana farin cikin hukumar tasu kan matakin da kwankwasawan suka dauka na bin doka ta hanyar shigar da wani korafin.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

810total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.