Faransa Za Ta Yi Amfani Da Jirage Masu Makamai Da Ke Sarrafa Kan Su

Yanzu haka dai kasar za ta fara amfani da jiragen masu makamai da ke sarrafa kan su, sabanin wanda tun da farko ta ke amfani da su wajen tattara bayanan sirri da gudanar da ayyukan sintiri.

Ministar tsaron Faransa Florence Parly, ta ce kasar za ta fara yin amfani da jirage masu sarrafa kan su wadanda ke dauke da makamai a maimakon wadanda ke gudanar da ayyukan sintiri da kuma tattara bayanan sirri kadai.

Ministar ta bayyana haka ne a lokacin da ta ke gabatar da jawabi a gaban taron shekara shekara da ya hada kwararri kan sha’anin tsaron kasar da ke gudana yanzu haka a Toulon kudun maso gabashin kasar.

Matakin na Faransa na a matsayin koyi ne ga sauran kasashe kamar Amurka, Isra’ila, Birtaniya da kuma Italiya da suka share tsawon shekaru suna amfani da irin wadannan jirage masu sarrafa kan su domin kai hare-hare kan abokan gaba.

Mafi yawa daga cikin wadancan kasashe Amurka ce ke kera masu jiragen samfurin Reaper, kuma suna fara amfani da makamai ne bayan samun izini daga Amurka.

Taro kan sha’anin tsaro da ke gudana wannan karo a garin Toulon da ke kudancin Faransa, na samun halartar kwararru sama da 400, da suka hada da sojoji, masu bincike da kuma wakilai daga kamfanonin kera makamai a Faransa.

Har ila yau taron na samun halartar babban kwamandan askarawan kasar Janar Francois Lecointre, da kuma shugaban kwamitin tsaro a majalisar dokokin kasar Jean-Jacques Bridey.

To sai dai taron ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Emmanuel Macron ta rage wa kasafin kudin tsaron kasar da sama da Euro milyan 800.

Asalin Labari:

RFI Hausa

552total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.