Farashin Raguna Ya Tashi A Kano Da Katsina- Bancike

Kwanaki uku kacal ya rage kafin bikin babbar sallah, farashin raguna ya tashi, ga kuma karancin masu siye kamar yadda masu sayarwar  suka koka.

Kamfanin Dillancin Labarai na NAN ya rawaito cewa farashin dabbobin yayi tsayiwar gwaman jaki a Katsina saboda karancin masu saye

Duk da cewa akwai yawaitar dabbobin a daukacin kasuwannin dabbobi dake cikin garin na Kano sai dai masu sayewar na mutukar korafin rashin ciniki.

Malam Sani Yaro wani babban dillalin raguna ne a kasuwar raguna dake unguwa-uku ya shaida rashin cinikin idan aka kwatanta da shekarar 2016 duk da cewa bai bayar da alkalumma ba.

Yaro ya kara da cewa duk da cewa babu ciniki amma farashin ragunan  ya daga da kashi 30 cikin dari idan an kwatanta da shekarar da ta gabata.

“Mutane na kokawa akan farashin ragunan, sai dai dole suyi la’akari cewa muma bamu siyo su da arha ba; don haka babu abun da zamu iya face addu’ar samun sauki nan gaba”.

Wani dillalin shi ma ya shaidawa kamfanin dillancin labaran na NAN cewa raguna 30 ya kawo Kano satin da ya wuce amma daga ciki bakwai kawai ya iya sayarwa.

“Nakasun da tattalin arziki ya samu duk shi ya jawo karacin cinikin, hakan kuma na shafarmu”, a cewar ta Maigari.

Ya danganta tashin farashin da hawhawar farashin sufurin kawo dabbobin daga Jamhuriyar Nijar.

Malam Buba Saidu shima wani dillalin dabbobin ne wanda ke kawo dabbobin daga Zamfara cewa yayi wasu kanzo ne kurum su taya dabbobin ba tare da sun saya ba.

“Muna addu’a samun ciniki kafin sallar domin mayar da raguna inda na siyo su Zamfara ba karamar asara bace gareni duba da dawainiyar da nayi.

Karanta:  Buhari ya Soke Taron Ministocin na Wannan Makon

“Abubuwa sun cukurkude ‘yan kwanakin nan, muna kira ga Gwamnatin Tarayya su yi wani abu cikin gaggawa don saukakawa talakawa”, a ta bakinsa.

Idi Sule, wani mai siyan dabbobi ne a Kasuwar Shanu ta Dawanau, ya shaida cewa zuwansa na biyu kenan kasuwar amma farashin yasa ya kasa siya.

“Nazo nan ranar Litinin amma ragon da na siya bara N20,000 yanzu shi ake siyarwa 30,000

“A shirye  na dawo yau  don ganin na sayi guda”, in ji shi.

Rasheed Ola, wani mai sayan dabbobin ne,  yayi burin ganin farasin ya fado sakamakon  karin shigo da raguna da yawa jihar.

Sakataren Kungiyar Masu Sayar da Shanu, Alhaji Dauda Sufi cewa yayi karami, da matsakaicin da kuma babban rago ana siyar dasu da tsada idan an kwatanta da da shekar da ta gabata.

Karami da matsakaici da babban rago a wannan shekarar ana sayar dasu akan N30,000, N50,000 dama N120,000 kwatankwacin N20,000, N35,000 da N80,000 a shekarar 2016”, a ta bakinsa

NAN ta rawaito cewa za a iya samun matsakaicin rago tsakanin N40,000 da N50,000 inda babba kuma yana kaiwa tsakanin N120,000 da N130,000.

Anyi la’akari cewa sakamakon hauhawar farashin dabbobin, musamman raguna, mutane musamman ma’aikatan gwamnati kan hada kudi ne su sayi shanu su rarraba naman a tsakaninsu.

Kamar yadda NAN ta rawaito a Babbar Kasuwar Maiadua dake jihar Katsina cewa karacin cinikin baya rasa nasaba da matsin tattalin arziki da kasar nan ke ciki.

Shugaban Kungiyar Dillalan Raguna ta kasuwar Maiadua, Malam Musa Rabe, cewa yayi bayan karacin masayan farashin ragunan ma yayi rugu-rugu idan an kwatanta da shekarar data shude.

Karanta:  Buhari ya je Daura bikin sallah

Yake cewa ragon da ake sayarwa tsakanin N70,000 da N80,000 shekarar da ta shude yanzu haka ana sayarwa tsakanin N50,000 da N40,000.

Shima ya danganta karacin cinikin sakamakon matsin tattalin arziki da kasar ke ciki, ya karawa da cewa da yawa daga cikin dillalan sai dai su mayar da ragunan su gida saboda karacin masu sayen.

Musa Maidoya dillali ne a barin sayar da shanu na kasuwar shima ya shaida karancin masu sayan dabbobin.

Yake cewa San N120,000 yanzu ana sayar dashi tsakanin N80,000 da N90,000,  ya kara da cewa ana kawo dabbobin daga Jamhoriyar Nijar amma dai kasuwar babu ciniki idan an kwatanta da shekar da ta shude. (NAN)

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

637total visits,82visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.