Farashin Ragunan Layya Sunyi Tashin Gwauron Zabbi

Yanzu haka Jamaa sun fara kokawa game da farashin ragunan layya, da yawan jamaa na cewa ko baya ga tashin farashin raguna haka kuma kudi sunyi wahalar

Yanzu haka Jamaa sun fara kokawa game da farashin ragunan layya, da yawan jamaa na cewa ko baya ga tashin farashin raguna haka kuma kudi sunyi wahalar samu.Hatta suma masu sayar da ragunan sun koka akan rashin kasuwa.

Yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke fara haramar shirye-shiryen sallar Layya – Yanzu haka farashin Raguna na kara tashin gwauron zabi, haka kuma jama’ar kasar na ci gaba da kokawa game da matsatsin rayuwa.

Isa Salihu Mai Rago na cikin dillalan raguna a Yola, Yace hasashe na nuna musu cewa bana akwai karancin Raguna lamarin da ya danganta da rashin kudi a hannun jama’a.

Kamar dai a jihar Adamawa, kusan haka lamarin yake a jihar Taraba, inda fatake da kuma masu saye ke kokawa.

Suma teloli da sau tari akan kai ruwa rana wajen cika alkawarin sun ce ba kasuwa, kamar yadda Safiyanu Umar wani tela ke bayani.

To sai dai yayin da cikin wasu ma’aikata ya debi ruwa na rashin albashi gabanin zuwan Sallar laihan shi ko,wani malamin firamare dabara yayi, tunda ance mai zurfin ido da wuri yake soma kuka.

Asalin Labari:

VOA Hausa

705total visits,3visits today


Karanta:  Magajin Garin Sokoto Danbaba Ya Ajiye Rawaninsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.