FBI Ta Ce Nakiya Ce Ta Fashe Cikin Masallaci a jahar Minnesota

Musulmi a masallacin Abubakar As Saddique dake birnin Minneapolis.

Babu wanda ya jikkata sakamakon bindigar da tayi a cikin masallacin da ake kira Dar al-Farooq.

A Minnestota, wani jami’in FBI yace wata nakiya ce hadin gida tayi sanadiyyar fashewa data auku jiya Asabar a wani Masallaci da ake kira Dar-al-Farooq dake birnin Bloomington.

Babu wanda ya ji rauni sakamkon wannan fashewa.

Jami’in na FBI Rick Thornoton,wanda shine jagoran masu binciken musabbabin wannan fashewar, ya gayawa manema labarai jiya Asabar din cewa, ” a wannan marra, abunda muka fi maida ha kali akai shine tabbatar da wanene ya dasa ta, kuma saboda me,” ya kara da cewa “Wannan hari ne na ta’addanci? shine abunda wannan bincike zai gano.”

Darektan masallacin Mohammed Omar, ya gayawa sashen Somalia na na Muriyar Amurka cewa, daya daga cikin masallatan ya ga wani mutum cikin wata mota akori kura aharabar maslalacin, kuma sai tayu yana da hanu a fashewar.

Lamarin ya auku ne da misalin karfe 5 na asubah agogon tsakiyar Amurka, watau misalin shida agogon Washington, karfe 11 na safe agogon Najeriya, Nijar Cadi da kamaru, watau 10 na safe agogon Ghana

Asalin Labari:

VOA Hausa

3511total visits,3visits today


Karanta:  Siera Leone: Zabtarewar laka ta kashe mutum 300

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.