Firaministan Congo Brazzaville Ya Ajje Aiki

FADAR Shugaban kasar Congo Brazzaville ta ce Firaministan kasar Clement Mouamba tare da daukacin ministocin gwamnati sun ajje mukaman su. Sanarwar ajje aikin dai tazo ne kwanaki bayan da shugaban kasar Dennis Sassou Nguesso ya bayyana shirinsa na kafa sabuwar gwamnati.

Sanarwar ajje aikin dai tazo ne kwanaki bayan da shugaban kasar Dennis Sassou Nguesso ya bayyana shirinsa na kafa sabuwar gwamnati.

A cewar shugaba Dennis Sassou Nguesso kafa sabuwar gwamnatin za ta taimaka wajen magance kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a shekarun baya-bayan nan.

Kasar Congo Brazzaville na daya daga cikin kasashen da suka dogara da sayar da man fetur, kuma faduwar farashin man a kasuwar duniya ta shafi kudaden da kasar ke samu.

Ya zuwa yanzu dai ba’a sanar da lokacin da za’a nada sabuwar gwamnatin ba.

Asalin Labari:

RFI Hausa

517total visits,1visits today


Karanta:  An Kafa Dokar Hana Fita a Houston Da Ke Fama Da Ambaliya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.