Fyade: ‘Yar shekara goma ta haihu a India

Yarinyar da akayi wa fyade a kasar Indiya wacce kotun kolin kasar ta hana a zubar wa da ciki a watan daya gabata mai shekaru goma ta haifi yarinya mace.

Sai dai har yanzu yarinyar bata san ta haihu ba sakamakon tun lokacin da cikin ya bayyana aka shaida mata cewar wani dutse ne a cikin ta wanda shine sanadin da ya sanya cikin nata yayi girma.

Jaririyar mai nauyin kilo 2.2 an haife ta ne a wani asibitin Caesarean a garin Chandigarh da misalin karfe 9:22 agogon GMT.

Mahaifiyar tare da jaririyar dukkan su suna cikin koshin lafiya. Sai dai mahaifiyar zata zauna a asibitin har akalla kwanaki goma masu zuwa domin kula da lafiyar ta.

An dai zargi cewar yarinyar an yi mata fyade ne a lokuta da dama wanda ake zargin dan uwan mahaifiyar ta ne yayi mata cikin wanda tuni jami’an tsaro suke tsare dashi.

Jaririyar da aka haifa mai tsahon watanni 35, zata zauna ne a bangaren kulawa da yaran da aka haifa wadanda basu kai watanni haihuwa ba.

A wani bangaren iyayen maijegon tuni sun bayyana cewar babu ruwansu da abinda za’a haifa wanda har a yanzu basu ko kalli jaririyar ba.

514total visits,4visits today


Karanta:  Saudiya Da Iran Za Su Kai Wa Juna Ziyarar Diflomasiya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.