Ganduje ya debi ma’aikatan lafiya 2,458 a Kano

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta debi ma’aikata 2458 domin cike guraben da babu kowa dama sababbin ma’aikata a jihar.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana hakan a jiya a yau a yayin raba takardun shaidar daukan aikin ma’aikatan a fadar gwamnatin jihar dake Kano. Sabbin ma’aikatan dai da aka dauka zasuyi aiki ne a shiyoyi daban-daban na kananan hukumomi 44 dake fadin jihar.

Gwamna Ganduje  ya bayyana cewa ma’aikata 2458 da gwamnati ta diba zasuyi aiki a bangarori lafiya kama daga asibiti izuwa ma’aikatun lafiya.

Ya kara da cewa daukar aikin yazo a dai dai lokacin da gwamnati ke bukatar su domin habaka bangaren lafiya ga al’ummar jihar Kano.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1535total visits,1visits today


Karanta:  Mutane Milliyan 9 a Afrika Na Iya Mutuwa Saboda Katse Tallafin HIV

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.