Buhari zai iya dawowa kafin karshen watan Agusta

Manyan shedu sun tabbatar da dawowar shugaban kasa general Muhammadu Buhari kafun karshen watan nan na August

Manyan shaidu sun tabbatar da dawowar shugaban kasa Muhammadu Buhari kafin karshen watan nan na August. Majiyar labarai ta daily times ta ce  in Allah Ya yarda da Muhammadu Buhari za ayi shagalin babbar sallah a Nijeriya.  Daya daga cikin mataimakin General Muhammadu Buhari yace duk an shirya yadda za a tarbi  shugaban kasa. Mataimakin yana magana da tabbacin  cewar yadda likitocin su ke kula da shi da kuma ci gaban da a ke samu. Majiyar ta ce matar shugaban kasa Aisha Buhari tayi kokari sosai akan dawowar mijin ta Nijeriya. Ya kara da cewa kada a manta da sadda suka ziyarshi shugaban kasa a ranar asabar shi da bakinsa ya tabbatar musu da cewa a shirye ya ke da ya dawo bakin aikinsa, abinda da kawai ake jira ita ce shawarar likitocinsa game da dawowar sa. Majiyar sun ce sun tabbatar da cewa shugaban Muhammadu Buhari  a shirye ya ke da ya gudanar da alkawarorin da ya dauka akan ci gaban Najeriya.

Majiyar tace a zuba ido a ga dawowar shi saboda ya ga alamomun ci gaban kasar bayan dawowar sa. Shugaban kasa ya kara da cewa a shirye ya ke da ya dawo kuma ya ci gaba da aikinsa, saboda ya yarda da Allah (S.W.T) da kuma addu’a, don haka duk wani makiyi ya je don kansa.

470total visits,1visits today


Karanta:  Bama Bukatar Wani Sabon Yakin - Ohanaeze Ndigbo

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.