Ghana Ta Lashe Kofin Gasar WAFU

Bayan nasarar lashe kofin, tawagar kwallon kafar kasar ta Ghana ta samu kyautar Dala Dubu 100.

Tawagar kwallon kafa ta kasar Ghana ta lashe kofin gasar kwallon kafa ta kasashen yammacin Afrika WAFU, bayan lallasa Super Eagles ta Najeriya da kwallaye 4-1, a wasan karshe da suka fafata jiya Lahadi.

Bayan nasarar lashe kofin, tawagar kwallon kafar kasar ta Ghana ta samu kyautar Dala Dubu 100.

Yayin gudanar da gasar a matakin rukuni, Najeriya ta lallasa tawagar kasar ta Ghana da kwallaye 2-0.

Yayin da Najeriya ke a matsayi na biyu a gasar cin kofin na WAFU, Jamhuriyar Nijar ce ta lashe lambar tagulla, bayan da ta lallasa Jamhuriyar Benin da kwallaye 2-1, ta kammala gasar kenan a matsayi na uku.

Asalin Labari:

RFI Hausa

759total visits,1visits today


Karanta:  Barcelona Na Neman Dan Wasan Gaba Na Manchester United Marcus Rashford Don Maye Gurbin Luis Suarez

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.