Giwaye da damusa sun hana mutane sakat a kauyukan Indiya

‘Yan kabilar Paharia da ke zaune a tsaunukan da ke yankin Jharkhand a kasar Indiya, sun kwashe kwanaki ba tare da sun runtsa ba.

Wata giwa ta tumurmushe a kalla mutum 15 har lahira a ‘yan watannin da suka gabata.

Daga can arewacin yankin kuma, wasu kauyaywa da ke zaune kusa da wani gandu ajiye Damusa, wato Tilibhit Tiger Reserve, wanda ke yankin Uttar Pradesh, sun kai wuya bayan da Damusa ta kashe mutane uku cikin mako daya.

Akalla mutum 16 ne damusa ta kashe a kusa da gandun tun daga watan Oktobar bara.

VK Singh, wani babban jami’i a sashen kula da gandun na Uttar Pradesh, ya ce, “Mun tura tawagar da za su yi wa dabbobin allura, domin su samu su mayar da su cikin gandun.”

Ya kara da cewa, “Mun san da cewa, mutane na cikin fargaba, lamarin ne na cike da kalubale.”

Akwai labarai da dama makamantan haka a kudanci da gabashin Indiya, inda ake da gandun ajiye dabbobi.

Ba dazuzzukan ne kadai lamarin ke shafa ba, har ma da mutane da ke cikin birane da kananan garuruwa ma sun soma fuskantar barzana daga Damusa.

Ma’aikatar kula da muhallan Indiya ta ce mutane 1,144 ne Giwaye da Damusoshi tsakanin watannin Afrilun 2014 zuwa Mayun 2017.

Kwararru sun ce alkaluman na iya wuce haka idan aka hada da wasu nau’in damusoshi da sauran dabbobin gandun dajin.

Alexandra Zimmermann, shugabar kungiyar IUCN, da ke sa ido kan muhallai na duniya, ta ce, “Matsalar tsakanin dabba da mutum na daya daga cikin manyan kalubalen da masu kula da muhallai ke fusknata, musamman ga manyan dabbobin da ke bukatar sa ido matuka.”

Karanta:  Jiragen Yaki: Amurka Ta Bukaci Bayani Daga Najeriya

Bayan la’akari da matukar raguwar da Damusa ta yi, gwamnatin Indiya sai ta kaddamar da wani shiri, watau Project Tiger Initiative, a 1970, inda aka kebe wasu wurare a gandun, kuma aka kafa dokoki hana farauta, wanda hakan ya taimaka suka sake karuwa kuma.

Kashi biyu na Damusoshin duniya na Indiya, inda alkaluman suka karu daga 1,700 har zuwa 2,200 cikin shekaru biyar din da suka gabata.

Ullas Karanth, shugabar sashen kimiyar dabbobi na Science-Asia Wildlife Conservation Society, ya ce matsalar da ake samu tsakanin dabbobi da mutane na aukuwa ne sakamakon cigaba da aka samu a gandun dabbobi a Indiya.

Ya ce, “Matsalar na kebe ne a wasu yankunan Indiya, da aka gyara muhallai kuma dabbobi suka karu, musamman ma Damusa.”

Na ziyarci gandun Damusar Sathyamangalam da ke Tamil Nadu a farkon wannan shekara.

A baya ba a san wannan gandun da yawan Damusa ba, sai a 2013 ne aka ayyana gandun a matsayin gandun Damusa.

A kalla Damusoshi 25 ne aka sani da zama a yankin, kuma suna karuwa.

Masana na ganin Damusoshin sun yi hijira daga Karnataka, jihar da ke makwabtaka, saboda cunkoson da ake samu a gandun da ke can.

Kauyawa a yankin sun ce suna ganin Damusa kusa da gidajen su, da tituna da kuma rafi.

An samu yawan tumurmusar Giwaye amma mutane na samun fargaba kan Damusa kuma.

Kusan kashi 60 cikin dari na giwaye a Indiya suke, inda aka yi kiyasin yawan su ya kai tsaknin 24,00 zuwa 32,000.

Masana sun ce bunkasa da aka samu na yawan al’umma ya katse yawan Giyawa, inda aka takura su a kananan yankunan, wanda hakan ke sa su far ma garuruwa da kayuka.

Karanta:  Wani mutum ya kashe matarsa saboda ta yi masa dariya

Misis Zimmermann ta ce ya kamata a sake nazari kan yadda za a kare Giwaye, da kuma bai wa ‘yan kauyen horo, kan yadda za su kaucewa dabbobin saboda su rika samun wucewa cikin sarari.

‘Samun daidaito’

Indiya na da mutane biliyan 1.2, kuma al’ummar na karuwa, wanda hakan ke sanya matsi ga gidaje da ma’aikatun kasar.

Mitsa Karanath ya ce, “A yayin da muke yunkurin samun cigaba a tattalin arzikin kasar, dole ne mu yi nazari kan tsare-tsaren da muka sa gaba.”

Ya kara da cewa “Gwamnati ba ta daukaki yin hakan ba, saboda suna hanzari wajen gudanar da wasu shriye-shiryen, ba tare da la’akari da matakan kariya wajen gini ba, wanda hakan ke da matukar damuwa a garemu.”

Ayyukan kare muhallai na da samun nasarar ta fannin ruwar da dabbobi suka yi.

Aikin da ke gaba dai yanzu shi ne samun daidaito a gasar da ake tsakanin mutane da dabbobi.

Lamarin dai baya zuwa da dadi ga wadanda ya ke shafa.

Wani da Damusa ta halaka danuwansa manomi cewa ya yi, “Mu dai so mu ke hukumoimi su kashe Damusar da ta ke kawo mana hari, kawai bukatar mu kenan, ba za mu daidaita kan komai da ya yi kasa da haka ba.”

Asalin Labari:

BBC Hausa

976total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.