Gobara Ta Kashe Daliban Islamiyya 22 a Malaysia

Makarantar Darul Quran Ittifaqiyyah, in da dalibai suka rasa rayukansu a wata gobara

Akalla daliban wata makarantar Islamiyya 22 da suka hada da malamai biyu sun rasa rayukansu sakamakon gobarar da ta tashi a dakin kwanansu da ke tsakiyar birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia.

Rahotanni sun ce, masu aikin kashe gobara sun yi nasarar kashe wutar wadda ta tashi da safiyar yau a Darul Quran Ittifaqiyyah, in da dalibai ke hadda Al-Kur’ani, yayin da hukumomin kasar suka bayyana gobarar a matsayin mafi muni da aka gani cikin shekaru 20.

Ministan ilimi Tengku Adnan Tengku Mansor ya ce, rashin hanyoyin fita daga dakin kwana daliban ya taimaka wajen mutuwarsu.

Shugaban ‘yan sandan birnin Amar Singh ya ce sun samu gawarwakin daliban menne da juna.

Kashi 60 na al’ummar Malaysia mai yawan mutane miliyan 30 Musulmai ne

Asalin Labari:

RFI Hausa

4005total visits,2visits today


Karanta:  An samu fashe-fashen bama-bamai a Maiduguri

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.