Guguwar Maria tayi Mummunar Barna a Dominica

Firaministan Dominica Roosevelt Skerrit, yace mahaukaciyar guguwar Maria da ta afkawa tsibirin, ta lalata duk wani abinda kudi ke iya saye.

Skerrit, yace guguwar ta dauke daukacin rufin gidajen dake tsibirin, kamar yadda mutanen da yayi magana da su suka shaida masa.

Firaministan ya bukaci taimakon kasashen duniya domin kaiwa jama’arsa dauki.

A yau Talata guguwar Maria da karfinta ya kai mataki na 5 ta aukawa Dominica da gudun kilomita 257 a sa’a guda.

Gugwar ta Maria na bin sawun ta Irma ne wadda har yanzu yankunan Carribea basu kammala murmurewa daga bala’inta ba.

A halin yanzu shugaban dake mulkin tsibirin Guadeloupe a yankin Caribbean ya bukaci kwashe mutanen dake fuskantar hadari daga guguwar Maria da yanzu haka ta dumfari yankin.

Sanarwar da ya bayar ta bukaci rufe daukacin yankunan da ake zaton suna fuskantar hadari domin kare lafiyar jama’a.

Shi ma dai tsibirin Guadeloupe dake karkshin ikon Faransa ya fuskanci hadari sakamakon guguwar Irma da aka samu makwanni biyu da suka wuce.

Asalin Labari:

RFI Hausa

924total visits,1visits today


Karanta:  Guguwar Maria za ta iya yin banna fiye da Irma- cibiyar binciken Guguwa ta Amurka

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.