Guguwar Maria za ta iya yin banna fiye da Irma- cibiyar binciken Guguwa ta Amurka

Guguwar ta Maria yanzu haka na gudun kilomita 150 cikin sa'a guda yayina ake hasashen cewa za ta iya kara karfi nan sa'o'i 48, kuma a cikin daren yau Litinin ne za ta isa tsibirin Leeward na yankin Caribbean. 18 septembre 2017.

Cibiyar binciken guguwa ta Amurka ta ce guguwar Maria za ta iya zamowa mafi hadari fiye da sauran guguwar da su ka gudana, a dai dai lokacin da ta ke gab da isa tsibirin Leeward na yankin Caribbean. Haka kuma guguwar ta Maria ka iya kara karfi cikin sa’o’I 48 masu zuwa yayinda da za ta isa tsibirin a cikin daren yau Litinin.

Wasu bayanan cibiyar ta NHC sun nuna cewa yanayin tafiyar guguwar da karfinta sun yi kamanceceniya da wadda ta gabace ta wato guguwar Irma.

A cewar bayanan, guguwar ta Maria na gudun kilomita 150 cikin sa a guda, yayin da ta ke tunkarar arewa maso yammaci, a dai dai lokacin da ake gargadin yankunan Guadeloupe da Dominica da St Kitts da Nevis da kuma Monsterrrat da ma Martinique kan su kasance cikin shirin fuskantar guguwar.

Ya zuwa yanzu dai yankunan da ke shirin fuskantar guguwar sun hada da Puerto Rico da tsibirin Virgin Island St Martin da St Barts da kuma Saba, sai St Eustatius da kuma Anguilla, wadanda kusan dukkaninsu basu kammala murmurewa daga banner guguwar Irma ba, wadda ta hallaka kimanin mutum 37 baya ga bannata dukiyar biliyoyin daloli.

Hasashen da cibiyar ta gudanar ya nuna cewa, za kuma a fuskanci ruwan sama mai karfi a yankunan daga yanzu zuwa daren ranar Laraba wanda kuma zai iya haifar da ambaliyar ruwa tare da zabtarewar kasa.

Asalin Labari:

RFI Hausa

559total visits,2visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.