Gungun mutane sun kashe sojan Nigeria

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane biyu dangane da kisan wani soja, Las Kofur Ayuba Ali da a ka yi jiya a garin Akwanga da ke jihar Nasarawa.

Mai magana da yawun rundunar ta jihar Nasarawa, DSP Kennedy Idirisu ne ya tabbatarwa kamfanin dillancin Najeriya, NAN, aukuwar lamarin a ranar Litinin a birnin Lafia.

Kakakin ya kara da cewa lamarin ya auku ne a lokacin da sojan ya banke wani dan talla da babur a Agwan Affi.

Rahotanni sun ce sojan na sanye da farin kaya a lokacin, kuma ya yi kokarin sasantawa da dan tallan amma lamarin ya tunzura wasu matasa a wurin, inda suka far masa da duka har sai da ya suma.

Idrisu ya ce daga baya sojan ya mutu a asibiti, kuma jami’an ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike a kan lamarin, kuma sun sha alwashin kama sauran wadanda ke da hannu wajen aikata wannan aika-aikar.

Wani wanda lamarin ya auku a gabansa, ya bayyana wa NAN cewa mutane sun kauracewa unguwar da abin ya faru domin tsoron abin da ka iya biyo baya.

“A halin yanzu akwai motoci guda hudu na sojoji a wurin, kuma sojojin na kama duk matashin da suka kama.”

Ya kara da cewa, mutane biyun da ‘yan sandan suka kama suna cikin wadanda suka kai sojan da aka kashe zuwa asibiti bayan da aka jikkata shi.

Asalin Labari:

BBC Hausa

536total visits,1visits today


Karanta:  An Sami Wani Dan Sanda Kwance A Mace A Kaduna

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.