Gurbataccen Kwai ya fara isa Asiya daga Turai

Badakalar gurbataccen kwan ta haddasa taya da jijiyoyin wuya tsakanin kasashen Turai

Badakalar yaduwar gurbataccen kwai da ta mamaye kasashen Turai 15, ta fara shafar nahiyar Asia, in da a baya-bayan nan matsalar ta isa Hong Kong.

Ministocin kasashen Turai da manyan jami’an kula da lafiyar abinci, za su gudanar da taro a ranar 26 ga watan Satumba, a wani yunkuri na kawo karshen zarge-zargen da kasashen nahiyar ke yi wa juna dangane da yaduwar kwan.

Matsalar dai ta haifar da tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Belgium da Netherland da Jamus, da suka kasance kan gaba a jerin kasashen da matsalar ta fi shafa.

Asalin Labari:

RFI Hausa

743total visits,1visits today


Karanta:  Biranen da Zasu Kare Yarjejeniyar Muhalli a Duniya

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.