Gwamna Tambuwal ya yi wa mutumin da matarsa ta haifi ‘yan hudu goma ta arziki

Gwamnatin jihar Sokoto ta bada tallafi ga Malam Lawwali mai shinkafa Illela, wanda matar shi ta haifi ‘yan hudu a makon da ya gabata.

Kwamishinan ma’aikatar jin dadin jama’a Alhaji Sirajo Gatawa ne ya gabatar da kayan ga iyalan ‘yan hudun a gidansu da ke cikin garin Illela.

A lokacin gabatar da kayan Kwamishinan ya ce Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ne ya umurce shi da ya gabatar da wannan tallafin biyo bayan sanar da shi da aka yi game da haihuwar.

Ya ce Gwamnan na iya kokrin shi wurin kula da jin dadin al’umma saboda duk lokacin da aka nemi ya bada tallafi ga wanda ke bukata yana badawa, ya bayyana sakon Gwamna na taya murnar samun wannan baiwar da Allahu ya yi musu tare da addu’a samun lafiya ga uwar da abin ciyar wa ga uban.

Gatawa ya mika tallafin kayan abinci da tufafin yara da na mahaifiyarsu da gadajen jarirai da katifu masu gidan sauro, da madararar jarirai da sauransu ga iyalan yaran mata ‘yan hudu.

Haka ma ya mika ma mahaifin yaran kudi naira duba dari biyar daga Gwamna Tambuwal. Shugaban karamar hukumar Illela ya godewa gwaman kan tallafin da aka bada,kuma ya hada matar da jamian kiyyon lafiya don bada shawarwarin kan yadda zaa kula da su .

Mal Lauwali da matar shi Shafa’atu sun nuna farin cikinsu da godiya ga Gwamana Tambuwal kan daukin da aka kai musu tare da rokon Allah ya biya shi.

Asalin Labari:

Rariya Online

825total visits,32visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.