Gwamnan Jihar Katsina Yace Yana Goyon Bayan Sake Fasalin Tsarin Gwamnatin Tarayya

Yayin da ake ta cece kuce game da sake fasalin tsarin Najeriya, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya shaidawa Sahabo Imam Aliyu ra’ayinsa game da wannan batu, inda yake cewa ya aminta da cewa ba shakka akwai bukatar rage wa gwamnatin tarayya karfi ko kuma ayyuka, to sai dai kuma idan za’ayi sai anyi la’akari da wasu abubuwa.

Yace kowane bangare na da irin nauyin da ya kamata a barshi ya dauka domin kowannensu yana da hanyoyin warware kalubalan dake gabansa.

Gwamna Masari yace ba abinda ya hada gwamnatin tarayya da gina rijiyar burtsatse, ko kuma makarantar Firamare da dai ire-iren wadannan ayyukan.

Sai dai kuma ya nuna cewa amma fa ba kuma za’a rage wa gwamnatin ta tarayya karfi bane ta yadda bata da iko fiye da sauran rukunin gwamnatoci ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

504total visits,1visits today


Karanta:  ‘Yan Bindiga Sun Kashe Sifeton ‘Yan Sanda Da Kwamandan ‘Ya Sintiri Sun Kuma Yi Awon Gaba Da Mata 2

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.