Gwamnan Jihar Neja Ya Kara Korar Kwamishinoninsa

Biyo bayan matsin lambar da gwamnan jihar Neja ke fuskanta daga jam’iyyar sa ta APC bisa sallamar da ya yiwa kwamishanoninsa, gwamnan, Alhaji Abubakar Sani Bello ya fito fili ya bayyan dalilan da suka saya yi waje dasu

Alhaji Abubakar Sani Bello yayi karin haske akan dalilan da suka sa ya kori kwamishanoninsa daga bakin aiki.

A cikin hirar da gwamnan yayi da Muryar Amurka yace kowace gwamnati bayan wani dan lokaci “kan yi tankade da rairaya”. Yace abun da aka saba yi suka yi domin su yi wasu gyare-gyare.

Dangane da gamsuwa da ayyukan kwamishanonin, gwamnan yace sun yi iyakar kokarinsu. Kowa da irin basirar da Allah ya yi masa, inji gwamnan, amma jikinsa ya gaya masa basu kai inda yake so ba. A cewarsa, a siyasance da bangaren aiki akwai gibi.

A halin yanzu gwamnan ya tura sunayen mutane goma sha biyar zuwa Majalisar Dokokin Jihar da yake so ya nada a matsayin kwamishanoni. Cikinsu akwai guda takwas daga cikin wadanda ya kora tun farko.

Sai dai wasu suna korafi akan sunayen da gwamnan ya mikawa majalisar. Alhaji Muazu Aliyu Jantabo shugaban kungiyar wasu matasa a yankin Lapai ya ce basu gamsu da wanda aka tura sunan sa daga yankinsu ba. Yace mutumin ya taba zama shugaban karamar hukumar su inda bai yi komi ba kuma da zara an tunkare shi, amsa daya gareshi, ita ce “ba kudi” abun da ya zama sunansa a Lapai maimakon sunansa na ainihi, Zakari.

Asalin Labari:

VOA Hausa

483total visits,1visits today


Karanta:  Cutar da ba a Sani ba ta Kashe Mutum 62 a Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.