Gwamnati Ta Dukufa Wajen Ceto Mutanen Da Aka Sace a Borno – Osinbajo

Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen ganin ta ceto malaman Jami'ar Maiduguri da ma'aikatan kamfanin NNPC da wani bangaren Boko Haram yake garkuwa da su.

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ta na kokarin ganin an kubutar da mutanen da ke hannun ‘yan kungiyar Boko Haram da aka kamasu a lokacin da suke binciken albarkatun man fetur a jihar Borno.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake kaddamar da wani kamfanin sarrafa shinkafa a birnin Arugungu da ke jihar Kebbi.

Mukadasshin shugaban kasan ya ce mutanen sun sadaukar da rayukansu domin yi wa kasa aiki saboda haka tsaro da lafiyarsu, ya rataya a wuyan gwamnati.

A makon da ya gabata ne ne ‘yan Boko Haram suka yi wa ayarin mutanen masu binciken man fetur daga Jami’ar Maiduguri da ma’aikatan NNPC kwantan-bauna a jihar Borno.

Lamarin ya kai ga asarar rayukan sojojin Najeriya da wasu ‘yan sintiri na sa-kai ko kuma ‘yan Civian JTF.

Asalin Labari:

VOA Hausa

636total visits,2visits today


Karanta:  Boko Haram sun dandana kudarsu

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.