Gwamnatin Najeriya Zata Maido Da Shingayen Tattara Harajin Bin Manyan Hanyoyin Mota

Tun lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo aka rushe shingayen karbar harajin hanya a duk fadin Najeriya saboda wai gwamnati bata amfana da harajin, saidai yanzu da za'a sake dawo dasu 'yan kasuwa ne zasu kula da su.

Ministan ayyuka, gidaje da lantarki Mr. Babatunde Raji Fashola ya fada cewa gwamnatin Najeriya za ta sake dawo da shingaye na karbar harajin gyaran hanya, watau Toll, a kan manyan titunan kasar.

A zamanin mulkin PDP da ya wakana tsakanin 1999 zuwa 2007 a karkashin shugabancin Chief Olusegun Obasanjo aka rushe irin wadannan shingayen bisa zargin cewa gwamnatin kasar bata amfana dasu. Sake dawo dasu zai ba gwamnatin damar samun kudin gyara hanyoyin.

Inji Babatunde Fashola an gano wurare 38 na guraben da aka rushe tun can asali inda za’a gina madakatar karbar harajin domin tabbatar da inganta manyan tituna. Za’a janyo masu zuba jari na gari da za su kula da titunan.

Tsohon ministan ayyuka Adesheye Ogunlewe wanda a lokacinsa aka rushe madakatun ya ce zai zama da muhimmanci gwamnati da ‘yan kasuwa su hada hannu a yi aikin. A cewar Ogunlewe idan ba’a yi hakan ba titunan ba zasu amfana da harajin ba.

Tsohon ma’aikacin gwamnati Tanko Iya ya ce dawo da madakatar abun da ya kamata ne saboda niyyar gwamnatin yanzu ce ta gyara hanyoyin kasar.

Shi ma shugaban direbobin manyan motoci na Najeriya Suleiman Dan Zaki ya nanata cewa hakkin manyan motoci ne su samarda hanya mai lafiya domin motocin ne ke kashe hanya.

Asalin Labari:

VOA Hausa

460981total visits,3visits today


Karanta:  An sanya James Ibori a kwamitin taron PDP

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.