Gwamnatin Najeriya Zata Taimakawa Jahar Nija Ta Wadata Afirka Da Abinci

Mukaddashin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ne ya bayyan haka a Minna fadar jahar Nija.

Gwamnatin tarayyar Najeriya zata hada karfi da gwamnatin jahar Nija dake arewacin Najeriya, wajen bunkasa harkokin noma, da zummar ciyar da kashi 50 cikin dari na al’umar nahiyar Afirka.

Mukaddashin shugaban Najeriya Parfessa Yemi Osinbanjo, shine ya bayyana haka lokacinda yake bikin bude taron bunkasa harkokin kasuwanci na kwanaki biyu a Minna, babban birnin jahar.

Osinbanjo, yace shi da Gwamna Abubakar Sani Bello, sun gudanar da shawarwari na fito da tsari mai kyau na cimma wannan buri.

Da yake magana Gwamnan jahar Abubakar Sani Bello, yace noma itace sahihiyar hanyar raya tattalin arziki, domin nan da shekaru 20 zuwa 30, kasashen yammacin duniya da suke kera motoci wadanda suke amfani da man fetur, zasu daina, su maida hankali wajen kera motoci masu aiki da wutan lantarki.

A nata bangaren, majalisar dattawan Najeriya tace zata kafa doka wacce zata saukakawa kananan manoma samun rance daga hanun bankuna inda ba’a za’a caje su kudin ruwa sosai ba.

Asalin Labari:

VOA Hausa

909total visits,1visits today


Karanta:  Ko Kunsan Kasar Da Ake Damawa Da Mata A Wasan Tamola?

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.