Gwamnatin Tarayya ta nemi kungiyar ASSU ta kawo karshen yajin aiki

Ministan Kwadago da Samar da Aiyuka, Dokta Chris Ngige, a jiya ya gana da Kungiyar Malaman Jami’a ta ASSU don samo bakin zaren yajin aikin da kungiyar ta shiga tun ranar Litinin din da ta gabata.

Ministan Kwadago da Samar da Aiyuka, Dokta Chris Ngige,  a jiya ya gana da Kungiyar Malaman Jami’a ta ASSU don samo bakin zaren yajin aikin da kungiyar ta shiga tun ranar Litinin din da ta gabata.
A sanarwar da ya fitar, Mataimakin Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar, Samuel Olowookere ya bayyana cewa ganawar wacce ta gudana a ofishin Ministan ta zama wani mataki na gano bakin zaren matsalar.
Ya bayyana cewa ganawar ta cimma matsaya dangane da gundar da bincike kan Naira biliyan 30 da aka baiwa kungiyar a shekarar 2010 tare da amincewa da biyan kungiyar basussukan da suke bi wata-wata tare kuma da ci gaba da bincike a hannu daya.
“Minista ya baiwa kungiyar ASUU tabbacin cewa ’yan Najeriya da gwamnati suna aiki tare don warware matsalar don ganin ba a samu wani tsaiko ko samun cikas a kalandar jami’o’in kasar nan”. Inji shi
Ya bayyana cewa ganawar za ta ci gaba da gudana gobe idan mai duka ya kai mu.
Asalin Labari:

Aminiya

611total visits,1visits today


Karanta:  'Yansandan Najeriya Sun Kama Masu Sace Mutane Tsakanin Kaduna da Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.