Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Hada Jihohi Uku da Layin Dogo

Ministan sufuri Amaechi ya fada a Sokoto gwamnatin tarayya na shirin hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo irin na zamani

Kokarin gwamnatin tarayyar Najeriya na hada jihohin Zamfara, Kebbi da Sokoto da layin dogo ba zai tabbata ba sai da amincewar Majalisar Dattawa a cewar ministan sufurin kasar.

A cewarsa tuni gwamnati ta tura bukatar zuwa majalisar.

Rotimi Amaechi wanda shi ne ministan sufuri a karkashin shugabanci Muhammad Buhari yace jihohin uku da ake son hadesu da layin dogo ko daga Katsina ko Kano suna cikin kudurin gwamnatin Buhari na hada duka jihohin Najeriya 36 da layin dogo a kokarinta na samar da ingantacen sufuri na layin dogon zamani.

Ministan na mai cewa idan “mun gama layin dogo na zamani daga Itakpe zuwa Warri da kuma na Legas zuwa Ibadan za samu adadin kusan kilomita 700 na layin dogon zamani a yammacin kasar ke nan”. Yanzu lamarin zirga zirga a yankin ya soma samun saukakawa.

Ministan ya ziyarci Sokoto ne inda ya yi jagoran babban taron majalisar sufuri ta Najeriya na wuni biyu. Taron da ya tattaro duk masu ruwa da tsaki akan harkokin sufuri na gwamnati da masu zaman kansu.

Wadanda aka zanta dasu sun bayyana jin dadinsu tare da cewa layin dogon zai yi babban tasiri.

Asalin Labari:

VOA Hausa

1079total visits,1visits today


Karanta:  Kallo Ya Koma Jihohi, A Yunkurin Samawa Kananan Hukumomi 'Yanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.