Hadiza Gabon ta Karyata Jita-Jitar Aurenta

A kwanakin baya ne aka yi amfani da shafin Facebook wajen yada jita-jitar cewa an daura auren jaruma Hadiza Gabon a Masallacin Juma’a na Sultan Bello da ke Kaduna. Duk da jita-jitar da ake ta yadawa, bai sanya jarumar ta shiga kafafen yada labarai don karyatawa ba, sai a kwanakin baya ta yi hira da Mujallar Fim, inda ta ce batun jita-jitar auren nata ya ba ta dariya.

Ta ce: “Da farko abin dariya ya ba ni, saboda lokacin da na fara ji ba ta riga ta yadu sosai ba. Daga baya na dauka wasa ne kamar yadda aka saba yi mana, yau a ce wane ya mutu, ko wance za ta yi aure, ko auren wance ya mutu, musamman ma a facebook. Akwai wanda ya kira ni daga Yola ya ce an fada masa sunan mijina Sambo.  Wasu kuma suka ce, a’a, ai mijin daga Yola yake; wadansu sun ce dan Kaduna na aura… babu dai irin maganar da ba a fada ba.”

Ta ce bayan jita-jitar ta baza gari abin bai bata mata rai ba, amma ta fara tunanin yadda za ta wanke kanta, kasancewar akwai lokacin da ta je wani shago wanke kai, kuma a ranar ta yi lalle a hannu da kafa, a lokacin da ake yi mata kitso a wani shago ne wata mata ta rika kallonta, bayan an fara hira sai ta tambaye ta wai ta ji an ce Gabon ta yi aure, “na ce mata a’a ban yi ba, sai ta ce bayan ta shigo har ta kalli lallen da na yi ya sa ta dauka da gaske ne.”

Karanta:  'Yan Kannywood mafiya yawan mabiya a shafukan sada zumunta

Ta ce a binciken da ta yi ta gano dalilin bayyanar wadansu hotuna da ta yi wa wata mata mai sana’ar yi wa amare kwalliyar ne, ya sanya aka fara yada jita-jitar auren nata.

“Bayan ta dauke ni hotunan ne aka sanya wasu a shafin Instagram, daga nan wadansu suka cire, sai kawai na fara ganin su a Facebook, ana cewa “Allah Ya sanya alheri”. “Yau za a daura wa jaruma Gabon aure.” Da dai sauransu.”
Ta ce wata ’yar uwarta daga kasar Gabon ta kira ta tana tambayarta me ya sa za ta yi aure ba tare da sanar da su ba, inda ta sanar da ita cewa jita-jita kawai.

Ta gode wa masoyanta wadanda suka turo mata da fatan alheri a lokacin da suka ji labarin an ce ta yi aure, sannan ta ji dadin addu’o’in da jama’a suka rika yi mata.

Asalin Labari:

Aminiya Trust

1766total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.