Haduran mota a bana ya halaka mutum 11,002 a Kamaru

A Jamhuriyar Kamaru mutane na kokawa kan yadda ake samun yawan hadarin mota a kasar, abinda suka ce kusan kullun mutane sama da 50 ne ke rasa rayukan su a sakamakon hakan.

Yawan hadarin mota  na faruwa ne saboda gurbatattun hanyoyin a mafi yawancin tituna a kasar, yawancin hanyoyin kasar Jamhuriyar Cameroon na neman jefa jama’ar kasar cikin halin kakanakayi. Musammam ma a irin wannan lokacin da ake ciki da daliban makarantun kasar ke komawa hutu.

A bisa kiyasin da akayi ance mutane sama da 50 ne ke rasa rayukan su a kullum a hanyoyin mota a kasar.

A bana kasar ta Kamaru ta fuskanci haduran mota fiye da dubu talatin, a yayinda fiye da mutane dubu goma sha daya suka rasa rayukansu a sakamakon haduran motoci.

Alamu sun tabbatar da cewa rashin kyawun hanyoyi ne ke haddasa wadannan yawan hadduran, bugu da kari direbobin da ake zargi da yin tukin ganganci, ko kuma shan abubuwa masu sa maye kafin su fara aiwatar da tukin.

Mallam Shu’aibu na daya daga cikin shugabannin kungiyar direbobin jamhuriyar ta Cameroon inda ya sanar dacewa ya yiwa Awal Garba bayanin cewa, ba shakka ana yawan samun hadari fadin kasar kuma daya daga cikin manya-manyan dalilan dake haddasa wadannan hadduran shine rashin kyawun hanyoyi duk ko da yake gwamnati na iya kokarin ta. Yace baya ga rashin kyawun hanyoyin, bugu da kari sunyi kanana inda kuma direbobi kanyi ta sharar gudu ba kakkautawa.

446total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.