Hajj: Ana Tsare Da Wani Mahajjaci Dan Nijeria Saboda Tsintar Wani Abun Da Ba’a San Komenene Ba A Harami

Ana tsare da wani mahajjaci dan Nijeriya a Makkah, Saudi Arabiyya bayan ganinsa da akayi ta na’urorin tsaro ya tsinci wani abu a kasa a cikin Harami.

Mahajjacin da har yanzu ba a bayyana sunansa ba ance jami’an tsaron sun tafi dashi wani gurin da ba a bayyana ko ina ne ba.

Yayin da yake zantawa da gidan rediyon Muryar Amurka, Ambasadan Nigeria a kasar Saudi Arabiyya, Alhaji Sani Yunusa cewa yayi har yanzu basu kai ga bin sawun lamarin ba, amma ya ja kunnen sauran Alhazan Nijeriya da su guji tsintar komenene a cikin kewayen Harami

“Nayi kokarin ganinsa har zuwa faduwar rana amma ban sami dama ba, yanzu haka ban san takameme a ina yake ba. Mun kewaye ofisoshin ‘yan sanda da dama amma bamu iya gano a ina yake ba. Don haka sai an ja kunnen mutanenmu kada su kuskura su tsinci komenene suka gani a cikin Harami don kare mutuncinmu da martabarmu,” a cewarsa.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

565total visits,5visits today


Karanta:  Iyaye na ba da 'ya'yansu ga Boko Haram – Sojin Nigeria

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.