Harin Numan: Ba Za Mu Yarda Da Kisan Mummuke Ba – Majalisar Musulmi

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Yola, shugaban hadin kan majalisar musulmi ta jihar, Ustaz Abubakar Sahabo Magaji, ya ce abun mamaki tun faruwar lamarin babu wani mutum ko guda da aka kama a kai.

Majalisar Hadin Kan Musulmi ta Kasa (Muslim Council), reshen jihar Adamawa, ta yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yiwa yara da mata Fulani makiyaya a Karamar Hukumar Numan tare da bayyana cewa kisan mummuke aka aiwatar a kan al’ummar Fulani Musulmi.

Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Yola, shugaban hadin kan majalisar musulmi ta jihar, Ustaz Abubakar Sahabo Magaji, ya ce abun mamaki tun faruwar lamarin babu wani mutum ko guda da aka kama a kai.

Sahabo Magaji ya yi watsi da batun cewa Fulani makiyayan sun shiga gonar manomin ne, inda ya ce wannan batun karya ne kawai da wadanda suka kitsa da aiwatar da kisan kiyashin suka shirya domin boye irin barnar da suka aikata.

A cewarsa, “ya zama wajibi gwamnatin jihar ta yi gaggawar kafa kwamitin shari’a domin binciken ko akwai gonar a wurin da Fulanin suke da inda aka yi wannan kisan. Mu a tsayinmu ba muna maganar Fulani aka kashe ba, maganar kisan, musulmi ne aka yiwa kisan mummuke, wanda mu ba za mu yarda da haka ba.

“Dama labari ya same mu wani Hakimi a Numan Mista Phones Garba, da ya samu shugabannin Fulani a garuruwan Kikan da Shafaren ya gargadesu da cewa su bar yankin, alhali sun zauna a gurin sama da shekara dari. Shugaban kauyen Kikan ya tabbatar da cewa idan fulanin suka ki barin yankin, za su turo da yaransu domin su tashe su daga yankin da karfin tsiya, wannan harin ya tabbatar da ikirarin shugabannin yankin” in ji Sahabo.

Shugaban majalisar hadin kan musulmin ya kuma yi barazanar cewa ba za su zuba ido suna ganin ana yiwa Musulmi kisa haka ba, a lokaci guda kuma hukumomin sun kauda kai sun ki daukan matakan da suka dace.

Karanta:  Ana ci Gaba Da Samun Raayoyi Mabanbanta Game Da Sake Kame Nnamdi Kanu.

“Muna son gwamnati ta gaggauta kafa kwamitin Shari’a ta yi bincike a kan wannan mummunan kisan rashin tausayi, kuma a gurfanar da mutanen da aka samu da laifi a gaban kuliya.

“Gwamnatin jihar ta tantance musulmin da suka rasa ransu da dunyoyinsu, kuma ta ba da kulawa ta musamman ga wadanda aka jikkata, hadi da duk irin jinyar da suke bukata.

“A bukata ta gaggawa muna son jami’an tsaro su dauki matakin bada ingantaccen tsaro ga duk wuraren da suke da hadari a yankin.

“Muna kira ga Karamar Hukumar Numan da ta dauki kwakkwaran mataki da ma wargaza wasu kungiyoyin ‘yan bangar da aka yi amfani da su wajan kai irin wadannan hare-hare ga Fulani Musulmi” in ji Sahabo.

Ya ce abun da ya faru ba fada tsakanin Fulani makiyaya da manoma bane kamar yadda kafafen yada labarai ke cewa, “kisan kabilanci da addini ne da wasu ‘yan bindigar Kabilar Bachama suka aiwatar a kan Fulani musulmi”, in ji shi.

Asalin Labari:

Leadership Ayau

2806total visits,84visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.