Hukumar EFCC Ta Bankado Miliyoyin Kudi Da Dillalan Mai Su Ka Ci

A cigaba da bankado kudaden Najeriya da wasu manyan barayi su ka sace, hukumar yaki da almundahana da gurgunta tattalin arzikin kasa (EFCC) karkashin Ibrahim Magu, ta sake gano wasu kudaden da aka yi kwana da su a bangaren mai.

Wakilin VOA Hausa a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ya aiko da rahoto cewa, “Jiya Talata Hukumar EFCC mai yaki da ayyukan karya tattalin arziki a Najeriya ta fadawa taron manema labarai a Kano cewa, ta kwato fiye da naira biliyan 328 daga hannun manyan kamfanonin dillancin mai guda tara a kasar da aka so yin rifda ciki akan su bisa hadin baki da Jami’an kamfanin mai na Kasa NNPC. “

Shugaban shiyyar Kano na Ofishin hukumar ta EFCC, Dr Adamu Hamisu Danmusa ya yi karin bayani wa wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari, da cewa da farko ana tsammanin kudin da su ka salwanta biliyan 40; amma da aka yi nisa da bincike, sai aka gano cewa kudin da ake binsu ya kai biliyan 349 da miliyan 118 da dubu 411 da 556 da digo 37.

Ya ce sun yi bincike sun gano man da aka ba kowanne daga cikin manyan dillalan man fetur da kuma yawan man da bai kawo ma. Y ace ta haka su ka san adadin da ake biyan kowanne su ka kuma umurce shi da ya mayar. Ya ce hatta shi kansa kanfanin NNPC an same shi da boye biliyan 39, wadanda a cewarsa tuni su ka kwato su ka saka a wani asusun a Babban Bankin Najeriya.

Asalin Labari:

VOA Hausa

538total visits,1visits today


Karanta:  Kotu Ta Amince Gwamnati Ta Rike Kudaden Diezani

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.