Hukumar SSS Ta Damke Wasu Kwamandojin Kungiyar Boko Haram

Hukumar tsaron farin kaya ta SSS a Najeriya ta ce jami’anta sun damke wasu manyan kwamandojin Boko Haram a jihohin Kano da Kaduna da Taraba.

Cikin wata sanarwa da hukumar SSS ta aikawa manema labarai, hukumar ta ce ta cafke wani babban kwamandan kungiyar Boko Haram mai suna Usman Musa a garin Sakwai dake karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Hukumar dai ta ce ta kama kwamandan ne tare da wasu mayakan Boko Haram, da suka hada da Isha Halidu da Ibrahim Dauda da Inusa Usman da Buhari Dauda da kuma Adamu Ibrahim. An sami makamai da wasu littattafan dake koyar da tsatstsauran akida tare da su.

Haka kuma hukumar ta ce ta damke wani babban dan Boko Haram a garin Bali dake jihar Taraba, mai suna Usman Halaji, dake ake masa lakabi da Abubakar Mubi, wanda ya tsere daga dajin Sambisa bayan dakarun Najeirya suka yi musu luguden wuta.

An dai kama wannan kwamanda ne yana yada akidar Boko Haram da kuma ‘daukar sabbin ‘yan kungiyar ta Boko haram.

An Kano hukumar ta cafke wani malami mai bayar da fatawa na kungiyar Boko Haram, Mallam Yusufu Isah, da kuma karin wasu mayakan.

 

Asalin Labari:

VOA Hausa

1633total visits,9visits today


Karanta:  Gwamnan Jihar Neja Ya Kara Korar Kwamishinoninsa

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.