Ina son dawowa amma sai likitocina sun sallame ni-Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan cewa likitocinsa ne za su yanke lokacin da zai dawo daga Kasar Birtaniya inda yake jinya tun ranar 7 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dage a kan cewa likitocinsa ne za su yanke lokacin da zai dawo daga Kasar Birtaniya inda yake jinya tun ranar 7 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.
Ya bayyana cewa yana ci gaba da murmurewa da samun koshin lafiya kuma yana bukatar ya dawo gida.
“Amma yanzu na gane muhimmanci yin biyayya ga dokokin likitocina a maimakon ni zan rika yin gabankaina. Anan likitoci ne ko da cikakken iko”. Inji shi
Mai Magana da Yawun Shugaban Kasa, Mista Femi Adesina a wata sanarwa da ya fitar, ya ce Shugaba Buhari ya yi furucin ne jiya lokacin da yake karbar bakuncin tawagar masu yada labaransa ciki har da Babban Mai Taimaka Masa a Harkokin Kasashen Waje a gidan Abuja da ke birnin Landan.
Tawagar wacce ke karkashin jagorancin Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammed ta kunshi Babban Mai baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Kafafen Yada Labarai da Wayar da Kai, Mista Femi Adesina da Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa Kan Kafafen Yada Labari da Wayar da Kai, Malam Garba Shehu da Miataimaka Masa Kan Kafafen Yada Labarai ta Yanar Gizo, Lauret Onochie da kuma Mai Taimaka Masa Kan Harkokin Kasashen Waje, Abike Dabiri-Erewa.
Adesina ya bayyana cewa yayin da tawagar ta bayyana farin cikinta kan murmurewar da shugaban yake yi sai ya amsa da cewa “ Ina son zuwa gida amma likitocina su ke da wuka-da-nawa kan haka. A yanzu na gwammace na bi dokokin da suka gindaya mani a maimakon na yi gaban kaina”.
Ya ce da suka tambayi shugaban ya ya ji kan maganganun da wasu ke yi kan rashin lafiyarsa, sai shugaban kasan ya ce ya na bin diddigin abubuwan da ke faruwa a gida inda ya yaba wa gidajen talabijin na Najeriya da sauran kafafen yada labarai da yadda suka rika sanar da shi abin da ke faruwa.
Asalin Labari:

Aminiya

848total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.