Iyaye na ba da ‘ya’yansu ga Boko Haram – Sojin Nigeria

Hukumomi a Najeriya sun ce akwai iyayen da suke bai wa ‘yan Boko Haram kyautar ‘ya’yansu musamman a yankin arewa-maso-gabashin kasar.

An samu bayanin hakan ne daga wasu ‘yan mata ‘yan kunar bakin wake da rundunar sojin kasar ta cafke, in ji kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman a wata sanarwa da ya aiko wa BBC.

Rundunar ta bukaci shugabanin al’umma musamman malaman addini da su rika fadakar jama’a “game da hadarin mika yara ga Boko Haram musamman saboda yadda ake amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake.”

Har ila yau rundunar ta yi Allah-wadai da iyayen da suke aikata hakan.

A baya-bayan nan an rika samun karin hare-haren Boko Haram musamman a garin Maiduguri na jihar Borno.

Abin da ya sa a makon jiya manyan hafsoshin sojin kasar komawa garin Maiduguri don ci gaba da yaki da kungiyar, bayan Mukaddashin Shugaban Kasar Yemi Osinbajo ya ba su umarnin hakan.

Asalin Labari:

BBC Hausa

640total visits,1visits today


Karanta:  Zama lafiya a Nigeria muke addu'a kullum - Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.