Jadawalin Fifa: Brazil ta doke Jamus

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta fitar da jerin sunayen kasashen da suka fi fice a kwallon kafa na watan Agusta, inda Brazil ta kawar da zakarun duniya Jamus a matsayi na daya.

Kasar Lionel Messi Argentina ta ci gaba da zama a gurbinta na baya, wato matsayi na uku, yayin da Switzerland ta zama ta hudu, sannan kuma Poland ta maye matsayi na biyar, matsayin da kasashen biyu ba su taba kaiwa ba.

Portugal din Cristiano Ronaldo ta rufto daga matsayi na hudu zuwa na shida, amma kuma kasar Alexis Sanchez, Chile tana nan daram a matsayin ta bakwai a duniya.

Colombia ce ke bi a baya a inda take ta takwas yayin da Belgium ke matsayi na tara, sai kuma Faransa wadda take ta goma a jerin gwanayen na duniya

Spaniya da Italiya dukkaninsu ba sa cikin goman farko a gawanyen kwallon kafar na duniya na Fifa na wannan wata na Agusta, kamar yadda jadawalin ya nuna, Spaniyar ce ta 11 sai kuma Italiyar ke bi mata baya, yayin da Ingila ke matsayi na 13.

Jerin Gwanayen Afirka

A Afrika kuwa inda Masar ke zaman ta daya a nahiyar kuma ta 25 a duniya, Najeriya ta matsa da mataki daya gaba a kan watan baya, inda yanzu ta zama ta 38 a duniya, sannan ta ci gaba da zama ta shida a Afirka, duk da kashin da ta sha a gida 2-0 a hannun Afirka ta Kudu, a wasan neman damar zuwa gasar cin kofin Afirka.

Jamhuriyar Dumokradiyyar Congo tana matsayi na biyu a Afirka ta 28 a duniya, yayin da Senegal ke matsayi na uku, sannan ta 31 a duniya, sai kamaru ta hudu a nahiyar, amma ta 35 a duniya.

A ranar 14 ga watan Satumba na wannan shekara ta 2017 za a fitar da jadawali na gaba na jerin gwanayen kwallon kafar a duniya.

Asalin Labari:

BBC Hausa

560total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.