JAMB ta Takaita Makin Shiga Jami’a Zuwa 120

Hukumar shirya jarrabawa ta rage makin shiga Jami’a zuwa 120 tare da rage makin shiga kwalejojin Ilimi da na fasaha zuwa maki 100.

Hukumar ta sanar da matakin ne bayan kammala wani babban taron masu ruwa da tsaki kan sha’anin ilimi a Najeriya a ranar Talata, inda aka yi nazari kan matsalar tare da daukar matakin.

Kafin daukar matakin, dalibai sai sun samu makin jarrabawar JAMB 180 zuwa 200 kafin samun shiga Jami’a a Najeriya.

Dalibai da dama sun fadi jarabawar da aka rubuta a bana, inda hukumar tace dalibai sama da budu dari biyar ne kawai suka samu maki 200 cikin dalibai miliyan 1 da dubu dari bakwai da suka zana jarabawar.

Sai dai kuma har yanzu Jami’o’I na damar kara yawan makin ga dalibai fiye da adadin da hukumar JAMB ta kayyade.

Asalin Labari:

RFI Hausa

851total visits,1visits today


Karanta:  Harin Numan: Ba Za Mu Yarda Da Kisan Mummuke Ba – Majalisar Musulmi

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.