Jami’ar Gusau Ta Bijirewa Matakin Hukumar JAMB

A bayan nan ne shugaban hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'i da manyan makarantu a tarayyar Najeriya Farfesa Is-haq Oloyede ya sanar da kayyade maki 120 a matsayin wanda za a rika bai wa dalibai gurbin karatu a jami'o'in kasar dashi

Wasu Jami’o’I a tarayyar Najeriya sun fara nuna halin ko’in kula kan matakan da hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi da sauran manyan makarantu ta kasar, JAMB ta gindaya, kan rage makin samun gurbin karatu ga dalibai zuwa maki 120 ga mai neman jami’a da kuma 100 ga sauran manyan makarantu.

Jami’ar tarayya ta Gusau a jihar Zamfara da ke arewacin kasar ta sanar da cewa sai dalibi ya samu maki 170 ne za ta bashi gurbin karatu sabanin 120 da hukumar ta JAMB ta kayyade a baya-bayan nan.

A wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na kasar, Jami’in yada labaran makarantar Malam Umar Usman ya ce jami’ar ta tsaida matakin ne la’akari da yawan daliban da suka nemi gurbin karatun, wanda kuma idan har ta amince da umarnin hukumar JAMB to fa bata da gurbin da zata debi ilahirin daliban.

Malam Umar Usman ya kara da cewa sama da dalibai 5000 ne yanzu haka ke dakon gurbin karatu, kuma gurbin dalibai dubu 1 da dari biyar kadai take da shi.

A cewar sa idan da za a agazawa jami’ar da abubuwan da take bukata babu shakka zata iya daukar dalibai fiye da yadda take dauka a yanzu.

Dama dai tun bayan sanar da matakin hukumar ta JAMB kan adadin makin da jami’o’in za su rika bai wa dalibai gurbin karatu da shi, an yi ta samun kace nace daga bangarorin jami’o’in da iyaye dama sauran masu ruwa da tsaki a harkar ilmi a Najeriyar.

Asalin Labari:

RFI Hausa

536total visits,1visits today


Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.