Jam’iyar Apc Barin Jihar Katsina Ta Zartar Da Goyon Bayanta Ga Buhari Da Masari A Zaben Shekarar 2019

Jam’iyyar APC a jihar Katsina jiya ta zartar da goyon bayanta ga shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Aminu Masari a matsayin ‘yan takararsu a babban zabe mai zuwa na shekarar 2019.

Yayin da yake yiwa manema labarai karin bayani a karshen taron majalisar zartarwa, shugaban jam’iyyar jihar Shitu S. Shitu yace, jam’iyar ta zartar da goyon bayanta ga shugaba Muhammadu Buhari da ya tsaya takarar kujerar shugabancin kasa.

Shi kuma Masari ya dawo a matsayin dan takarar gwamnan jihar a zabe mai zuwa na shekarar 2019. Ya kara da cewa zartar da matakin ya biyo bayan irin kyawawan shirye-shiryen mutanen biyu wandanda suka inganta rayuwar al’umma.

Yace manufofin gwamnatin Buhari da Masari a bude suke kuma sun cimma nasarori masu dinbin yawa.

Asalin Labari:

Muryar Arewa, Daily Trust

1440total visits,1visits today


Karanta:  APC Ta Kira Aisha Alhassan Dangane Da Maganganun Da Tayi Akan Buhari

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.