Jam’iyyar APC ta mika sunayen ‘yan takara daga Zamfara

Hukumar zabe wato INEC ta ce tana nan kan bakanta game da kin amincewa da sunayen ‘yan takarar jam’iyyar APC daga jihar Zamfara, duk kuwa da wani hukunci da kotu ta yanke a kan al’amarin.

Hukumar ta ce a ta ta fahimtar umarnin kotun yana nuni ne da cewa kowa ya tsaya a kan matsayin da ya dauka.

Wata babbar kotu ce a jihar Zamfara ta bayar da wani umarni na wucin gadi, wanda ya hana hukumar zabe ta kasar INEC da jam’iyyar APC haramta wa ‘yan takarar jam’iyyar na kujerun gwamna da majalisar dokoki ta tarayya da na jihar, shiga babban zaben da za a yi a badi.

Wasu shugabannin reshen jam’iyyar APC na jihar Zamfara ne suka shigar da karar, bayan hukumar zaben ta hana jam’iyyar gabatar da sunayen ‘yan takarar na ta na jihar, saboda rashin gudanar da zabukan fitar da gwani.

8721total visits,6visits today


Karanta:  Shekaru Biyu Da Mulkin APC: Gwamnati Ba Ta Yi Aikin Komai Ba — Hassan Hyat

Leave a Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.